TAKOBIN ZARMA

TAKOBIN ZARMA
Written by Abdul King Article
A birnin ganya, shekaru da dama DA suka shude, anyi wani
gagarumin sarki, mai karfin iko da tarin dukiya, wannan sarki ana kiransa da suna Nalim, Nalim
nada magaji daya wato yarima Haras sai kuma matarsa wato sarauniya Munayyat. Sarki Namil na mutukar ji da wannan da nasa hakan yasa ya nuna masa kowace irin
kauna, yarima ya kasance kyakkyawa, ga ji da kai, hakan yasa
Yan matan birnin ke shawarsa, amma shi ko a jikinsa, ba
wadda ta masa a cikinsu
Wata Rana da dare, kawai sai yarima yaji Ana buga tambarin
yaki, take ya tashi a tsammaninsa hari aka kawo musu, to
bayan ya fitone sai shugaban dakarun ya masa bayani cewa,
barayi ne suka shiga masaurautar, anga sun fito da jaka amma
ba asan ko meye a ciki ba, to anan yarima ya musu umarni
dasu kara bada tsaro zai shiga ciki yaga abunda aka dauka,
bayan ya shiga ne ya bincika iyakar kokarinsa amma bai ga
abu mai muhimmanci da aka dauka ba, yana cikin bincikawa
gabansa ya fadi ras, to anan ya duba bai ga takobin zarma ba,
wani takobi ne mai asali da mahaifiyarsa ta bashi kafin ta rabu
da abbansa, ta masa wasiya cewa kada ya rabu da takobin
komi rintsi, to anan ya fara tunanin mahaifiyarsa,a lokacin data
bashi takobin yana yaro, kawai sai ga abbansa yazo gunta,
daga nan suka fara wata magana sai dai bayajin abinda suke
fadi domin hankalinsa na ga takobin, kawai sai ya ga
mahaifiyarsa ta fita cikin fushi ta hau doki ta nufi kofar fita
garin, daga nan abbansa ya fara kiranta amma ko juyowa
batayi ba balantana ta kalle shi, kawai sai yaga abbansa ya
rungumeshi yana kuka, wannan ya dunguzumar da hankalinsa,
haka ya fara tambayar abbansa, baba meyasa kake kuka?
menene amfanin takobin da mama taban? kuma meyasa ta
tafiyarta kana kiranta amma bata dawo ba? sarki dai ya cigaba
da kukansa batare da bashi amsar wadannan tambayoyi ba.
Wannan tunani na yarima ya katse bayan da yaji shigowar wani
a cikin dakin, dubawarsa keda wuya sai yaga ashe abbansa ne,
kada ka damu yarima, gobe Zan sa a bincika kowane gida
dake wannan birnin domin ganin takobinka, duk da bansan
amfaninsa ba a wurinka, gama fadin haka keda wuya sarki ya
juya ya tafiyarsa, anan mamaki ya kashe yarima: to ya akayi
yasan da cewa an sace takobin alhali bacci yakeyi, kuma alhali bai da masaniyar takobin to ya akayi yasan da hakan?
wayewar gari keda wuya dakaru suka shiga aikinsu, gida gida,
ko ina shiga ake ana bidar takobin, a cikin haka ne suka shigo
wani gida tare da yarima, wannan gida dai ya kasance na mace
ne tare da yarta, yarima yayi mamaki sosai domin duk
maganar da akayi matar ke amsawa, ita diyar dum take bata
magana, yarinyar ta kasance kyakkyewa abar kallo, saboda
haka yarima ya tambayi sunanta, kawai sai ya ga ta kalle shi ba
tare da yin magana ba, daga nan sai mahaifiyarta tace: ranka
shi dade ai bata magana, to me yasa? yarima ya tambayeta,
kawai sai ya ga ta done Kai ba tare da bashi amsar tambayar
daya Mata ba, to bayan sun gama bincike sai suka koma gida.
A wannan dare dai yarima na cikin wani hali na tunani, saboda
haka sai ya fito ya fara yawo a cikin masarautar domin samun
abun debe kewa, cikin wannan yawo da yakeyi ne ya shigo
wani daki mai yawan karikitai, ya dubi dakin daga sama har
kasa ya gane cewa kamar bai taba shigowa a ciki ba, wannan ya
kara tabbatar mai da cewa masarautarsu nada fadi, anan yaga wani
akwatin zinare yana walkiya kai kace
hasken wata, take ya nufi wurin da nufin daukar akwatin, cikin
mamaki kawai sai yaga akwatin yaja da baya kamar ana jansa,
haka yarima yayi ta kokarin daukarsa, amma akwati yaki bari
ya daukai, cikin fushi yarima yayi wani tsalle da nufin dahe
akwatin amma Ina, cikin sauri akwati ya shige wani daki mai
duhu ya boye, daga nan yarima ya bishi a guje, yarima na
shiga dakin kawai sai ya ga duk fitillu sun kawo, cikin rashin
sani ya taka wani wuri, ashe tarko ne, kawai sai ya ga mashi ya
fito daga wani lungu da zimmar sokeshi, a wannan lokaci
yarima bazai iya kare kanshi ba, haka yayi tawakkali ya mika
wuya, kadan ya rage mashin ya soke shi kawai sai yaga wata
garkuwa ta karfe ta fito ta tare mashin, a nan take garkuwar ta
mayar da mashin inda ya fito, sannan ta koma wurinta, wannan
abu ya daure ma yarima Kai, anan ya Fara tunani shin mafarki
ne yake ko meke faruwa wai, kawai sai yaga akwatin ya kawo
kansa wurinsa, anan ya bude akwatin, kawai sai yayi kicibis da
wasika, take ya fara karanta wasikar kamar haka:
AMINCI YA TABBATA A GAREKA YA DANA, WANNAN WASIKA
CE DAGA MAHAIFIYARKA, MAI KAUNARKA, WATO KA SANI
CEWA: DUK WADANNAN ABUBUWAN AL AJABIN DAKA GANI
A CIKIN WANNAN DAKI NINA SHIRYA SU, BA DON KOME BA
SAI DON KADA WANI YA KARANTA WANNAN WASIKAR, NA
KASANCE MAI HIKIMAR KIRA, SABODA HAKA NA TANADI
WADANNAN TARKUNA, IDAN KA LURA AI AKWATIN DAKAGA
YANA TAFIYA YANADA KACA A DAURE, HAKAMA MASHI DA
GARKUWAR DAKA GANI, SABODA WANNAN HIKIMAR CE
MAHAIFINKA YA AURE NI, KUMA NASAN DACEWA A YANZU
SHEKARARKA ASHIRIN CIF, BAKO SHAKKA KANA CIKIN
WANI YANAYI NA SON SANIN AMFANIN TAKOBIN DANA
BAKA,DA KUMA MEYE MAKASUDIN TAFIYATA, WATO
TAFIYATA NADA MUHIMMANCI A GAREKA, DA KUMA
MUTANEN BIRNIN GA BAKI DAYA, NA GANO CEWA BABANKA
NADA WANI SIRRI, KUMA WANNAN SIRRIN KAN IYA ZAMO
SANADIN MUTUWAR KOWANE MAI RAI A WANNAN BIRNI,
SABODA HAKA NAYI WANNAN TAFIYA MAI HADARIN GASKE
DOMIN GANO KO WANE SIRRI NE,DA KUMA YADDA ZAN
KARE MUTANEN BIRNIN, AMMA BAN SO KA GAYA MASA
KOME AKAN HAKA, SABODA HAKA YANZU INA BUKATAR
TAIMAKONKA, INASON KAJE BIRNIN GANDUJE, ACIKIN
GARIN ZAKA GA WATA YARINYA MAI SUNA HALIRAT, TO
ITACE ZATA BAKA SAKONA, KA HUTA LAFIYA
To bayan yarima ya gama karatun wannan wasika, kawai sai
yaji bakin cikinsa ya yaye, cikin jin dadi ya koma dakinsa,
shigarsa keda wuya sai ya ga wata yarinya a zaune tana
jiransa, bakowa ceba in banda wannan yarinyar da mahaifiyarta
tace bata magana, kawai sai yaga taja hannunsa, suka yita
tafiya har suka isa gidansu, yarima yayi mamakin abinda yasa
ta kawoshi gidansu, to bayan ta zaunar dashi kawai sai ga
mahaifiyarta tazo, a take ta Fara yi masa bayani cewa: ai ni
NASA ta kiraka, wato jiya na fita bayan gari sai nayi arba da
wasu mutane sanye da kaya bakake, to na gansu dauke da
wani takobi mai walkiya, kuma naji a hirarsu suna cewa gobe
zasu wuce birnin ganduje, soboda haka naga Bari in gayama
watakila idan kaje ka dace, wannan labari ya mutukar tayarma
da yarima hankali, domin wannan birni shine mamarsa tace
yaje, to kafin yayi sallama dasu sai yace ,amma Zan so ki
gayamin sunnan wannan kyakkyawar diyar taki, to anan
yarinyar ta kalle shi tare da yin murmushi, an an mahaifiyarta ta
Fara magana da cewa,ai duk abunda ka fadi tanaji, mayarwa
kawai bazata iyaba, sunanta halirat, anan gaban yarima ya fadi,
to kada dai ace itace wadda nake bida, ya fadi a cikin zuciya,
haka dai yayi sallama dasu ya nufi gida.
Washe gari tun da safe ya dauki niyar zuwa birnin ganduje,
mahaifinsa yayi ya gaya masa inda zai nufa amma yaki, haka
yarima ya hau dokinsa ya nufi hanyar fita daga birnin.

TAKOBIN ZARMA 2
A lokacin da yarima ya fita daga birnin
ganya, kwanci tashi har ya iso birnin ganduje, to a bakin kofar
garin ne yaga mamaki, domin wata yarinya ya gani tana yaki da
wasu katta, kome ya gama su dai oho, saboda tsananin bala in
yarinyar suka yarda makamai suka gudu, to a cikin makaman
da suka yarda ne yarima yaga wani takobi mai walkiya, anan ya
matso domin ya gani, aiko sai ya gane cewa takobinsa ne
daya fito nema, kawai sai yaga yarinyar ta dauki takobin, anan
yasha gabanta yana mai cewa takobinsa ne ta bashi, anan tayi
mumushi tace, to karfin ka ya kwatar ma, cikin fushi yarima
yakai mata wani irin naushi, take suka kacame da yaki, ashe
duk abinnan dake faruwa dakarun dake gadin kofar garin suna
nan suna kallonsu, anan suka sheko da gudu suka kamasu
suka wuce dasu wurin sarkin garin, to da sarki yaji abinda ya
hadasu, take ya bukaci ganin wannan takobi, koda aka bashi
sai yayi dariya yace: shekarata goma ina bidar takobin zarma
amma sai yau ya iskoni har gida, anan sarki ya bada umarni
akai su gidan yari a rufe. To bayan da aka kaisu gidan yari,
anan yarima yama wannan yarinyar kallon tsaf, sai yaga tayi
kamada halirat din daya baro a ganya, to a nan ya fara yi mata
magana, amma kinada kanwa a wani gari ko? Ta amsa masa
da aa, to kaifa, ko kaine yariman ganya? Anan yace E, nine,
daga nan saita fara basa labari cewa: Sarauniyat Munayyat wato mamarsa
ta bata umarnin cewa tazo birnin ganduje zata hadu da yariman
ganya, to idan ta hadu dashi ta gaya masa cewa ya iskota ita
sarauniyar a dajin dake gabanin birnin ganya, wannan labari
yasa yarima ya gane cewa wannan sarauniya itace
mahaifiyarsa, ita kuma wannan yarinyar itace halirat da akace
yazo wurinta ta bashi wannan sako, haka suka cigaba da tadi sai
kace wadanda basuyi taba fada ba. Washe gari aka fiddo su,
anan aka kawosu tsakiyar wani fili mai tarin jama a, kamar
suna wata bauta, sai kuma ga wasu mutane daure, anan aka
fara yanka wadannan mutane. akayita haka
har aka kawo ga halirat, wani kato na rike da gatari, anan ya
daga da nufin rabata gida biyu, yarima na ganin haka sai yaji
karfinsa ya dawo, anan ya zubar da dakarun dake rike dashi,
take yayi wani tsalle ya buge gatarin, hakan yaba halirat damar
kubcewa, cikin sauri ta dauki gatarin ta raba mutumin gida
biyu, daga nan kuma ta nufi wurin sarki da nufin amsar takobin
zarma dake rataye a kugunsa, to a wannan lokaci fiye da
dakaru dubu suka rufar mata da nufin kare martabar sarki,
jama a suka wangame baki suna kallon wannan al amari,
domin ba a taba samun sadaukan da suka taba yin haka ba,
suna cikin haka sai sukaji haniniyar dawakai, anan suka ga
wata runduna ta mayaka, take gaban yarima ya fadi, domin a
tsammaninsa duk mayakan sarkin ne, sai dai ba haka ba, daga
isowar wadannan mahaya dawakai, sai suka hau mutanen
wannan sarki da sara, haka yaba halirat damar kwace tokobin
daga sarki a saukake, to koda mahaya dawakan suka gama da
dakarun wannan sarkin, sai suka juya suka fita,to anan ne
yarima ya gane cewa shugabansu kamarsu daya dashi, wato kamar an tsaga kara. a nan
ya shiga kogon tunani, wai dama inada dan uwa ban sani ba?
Cikin hanzari dai ya samu doki ya haye, itama halirat ta
biyoshi, a nan ya dauketa ya aza saman dokin sannan ya nufi
kofar fita birnin, shi kuma sarki suka barshi da bakin ciki. Sun
yi gudu iyakar gudu, daga nan suka iso wani daji, basu dade da
zaunawa ba sukaji motsi, koda yarima ya duba sai yaga ashe
halirat din ganya ce tare da mahaifiyarta, anan yayi mamakin
kome ke tafe dasu, cikin shessheka ta gaya masa cewa birnin
ganya ya fadi, domin wasu halittu suka shigo masu kamada
dan adam, sai dai munana ne, kuma sunada fuka fuki,kashe
mutanen garin kawai sukeyi, to anan ta ankara da halirat
yarinyar dake tare da yarima, anan ta sheko ta rungumeta tana
murna, anan ta gayama yarima cewa: wannan yarinyar da kake
tare da ita diyata, itace halirat din gaskiya, ita wagga da bata
magana sunanta nusaiba, amma ka gafarceni yarima dana yima karya domin lafiyarta lau tana magana mun dai yi hakane don gudun matsala. saboda bacewarta saina
dinga kiran nusaiba a matsayin halirat, anan dai yarima ya
umarcesu dasu cigaba da dubawa ko zasu ga sarauniya, domin
a cikin wannan dajine tace ya sameta, haka ko akayi, suna
cikin tafiya ba sassuci sukaci karo da wasu tantuna, anan sukaji
magana a bayansu, sannunku da zuwa, juyawar da zasu yi sai
sukaga mace a gabansu, to a nan halirat ta ganeta, bayan
sarauniya tayi maraba dasu, saita fara basu labarin tafiyar da
tayi, da kuma sirrin sarkin ganya data samo, wato ku sani
cewa: sarkin ganya yana cikin wata kungiya dake satar kananan
yara suna mayar dasu wasu halittu munana masu fuka fuki,
sukan turasu yaki ga duk sarkin dayaki basu abinda sukeso,
sukan yi amfani da tsafi wajen sauya ma wadannan yara
halitta, jagoran wannan kungiya shine sarki talim, kafin
sarauniya ta cigaba da bada labarin sai taga suna hamma
alamar sun gaji, daga nan sai tace, to gobe zan iyar da baku
labarin wannan tafiya danayi da kuma abinda na gano a ciki.
TAKOBIN ZARMA 3
Written by Abdul King Article
To anan ne Sarauniya ta nuna musu inda zasuyi bacci har zuwa da safe ta iyar da basu labarin. Ai kuwa su yarima na shiga tantinsu suka fara bacci kamar bazasu tashi ba. A haka sukayi kwanciyarsu ba tare da shaukin kome ba har sai da safiya ta waye. To anan ne sarauniya ta fara tadasu da kanta. Firgigit yarima ya mike a tsorace domin a tsammaninsa hari ne aka kawo. Sarauniya murmushi tayi da taga alama kamar danta ya tsorata.
” Kada ka damu dana, ba abunda ya faru, yanxu ku gaggauta shiryawa sabida bamuda lokaci kuma ya kamata ace mun kammala abinda ke gabaninmu.” Daga nan sai yarima ya fita cikin tantin yana hamma, ai kuwa yana fita sai kallo ya zamo masa sabo domin wasu tantuna ne ya gani da yawa kamar da alama cewa sune dakarun dake gadin sarauniya. Haka yarima yaci gaba da kallon filin, abun ya kasance gwanin ban shaa wa irin yadda yaga wasu daga cikin dakarun sai wasannin suke da takubba wasu komu dambe, kowa dai sai sha anin gabansa yake. Wasu kuyangi ne mata suka kawo wa yarima wani dan koko wanda a cikinsa akwai ruwa. Yarima komawarsa yayi gefe har sai da ya tsaftace jikinsa sannan ya koma cikin tantinsa. Anan ya isko abincuccuka kala kala. Su biyar suka zauna wato dashi da mahaifiyarsa sarauniya, sai halirat da nusaiba da kuma mahaifiyarsu. Anan suka shiga kalaci ba sassauci sai da kowanensu ya cika tumbinsa sannan sai sarauniya tayi gyaran murya domin ci gaba da basu labarin jiya:
” Kamar yadda na fada muku cewa na gano sirrin mijina Nalim wato sarkin Ganya. Bako shakka yana cikin wata kungiya shida wasu sarakunan duniya su goma. Ita wannan kungiya tasu sun kafata ne ba don komi ba sai don su cimma burinsu na samun matsayin da babu wani mai irinsa a duk fadin duniya, suna so sufi kowane sarki tarin dukiya da kuma tarin mayaka. Kuma sunaso sufi kowane sarki izzar mulki da mata kyakkywa. Kuma suna so su dinga juya duniya yadda sukeso ma ana su dinga baiwa kowane sarki na duniya umarni. Umarni wanda dole abi ko kuwa jiki yayi tsami. To a cikin bincikensu na tsafi sai suka samu bayani cewa idan har sunaso su samu wadannan abubuwa da suke nema dole sai sun samu wasu dakaru da akewa lakabi da Laznun. Su wadannan dakaru yadda ake samunsu shine ta hanyar kananan yara maza ko mata. Idan suka kama kananan yara zasu ajiyesu cikin wani daki nasu na tsafi har sai sunyi kwanakin casa in. To a cikin wadannan kwanaki ne wasu ifritan aljnnu zasu dinga shiga jikin yaran suna zuke musu jini suna mayar musu da jinni marar kyau. to da an kwan casa in ana bude dakin sai aga yaran sun canza kammani sun koma manya manya masu girma kuma mummuna. Fuka fuki biyu zasu fito musu daga nan kuma sai su fita cikin hayyacinsu yadda duk abunda aka basu umarni zasuyi. Su wadannan dakaru na laznun sun kasance masu karfin gaske yadda kome jarumtakar mutum idan sukayi arangama dashi to sai sun kaisa kasa.

Wadannan sarakunan su goma sun yi amfani da wadannan dakaru nasu sun yi ma sauran sarakuna barna tare da amshe musu dukiyoyi,mataye, da birane. Akan wannan dalili yasa yanxu haka mafi yawan sarakuna na duniya suna tsoron wadannan sarakuna don gudun kada su rasa sarautarsu. Akan wannan dalili yasa duk abunda akace suyi to dole suyi don dole ba don sun soba. Kuma yanxu haka suna gab da azawa sauran sarakuna harajin karfi da yaji. Kamar yadda na fada muku a jiya shugaban wannan kungiya shine sarki Talim na birnin Asmariya.
” To amma umma idan hakane ya akayi wadannan halittu suka afkawa birnin mu da yaki. Ai bai kamata ace sun yaki abba ba tunda ya kasance a cikin kungiyarsu. ” Haka yarima ya fada cikin damuwa.
” Yaro man kaza.” Haka sarauniya ta fada tana duban danta yarima. ” To ai baka bari na iyar da labarin ba balantana kaji. Wato ka sani shi abbanka ya kasance mutum mai tausayi da kuma son kyautatawa. Dama sarki Talim ne ya masa tayin shiga kungiyar shi kuma ya aminta ba tare da sanin abunda suke ciki ba. To bayan ya shiga ne sai yayi niyar fita domin shi bazai yarda da irin wannan zalunci da suke yiwa sauran sarakuna ba. To ga kaidar wannan kungiya idan aka shiga ba a fita. Wannan shine dalilin da yasa suka samu sabani mai yawa har takai a yanxu suna kokarin amshe masa birni.”
” To umma idan hakane yanxu wace hanya zamubi na ganin mun ceto birninmu tare da sauran birane.? ” yarima ya tambaya
” Hanya biyu ne, wato da farko dai…..” To kafin ta iyar ne sai sukaji ihu da kururuwa na mutane. Anan suka tashi da sauri suka fita. Suna fita suka tarar da cewa dakarun sarki talim ne wato Laznun. Sune suka kawo hari sai faman kashe mutane suke. ” Ina takobin zarma?” Sarauniya ta tambaya. Anan halirat ta jefo mata shi. Daga nan sai ta cabesa da hannu daya. ” Ku sani cewa sunxo neman wannan takobin kuma bako shakka sarki talim ne ya aikosu. Ku biyoni. ” Anan sarauniya ta fara gudu suna binta har sai da suka kawo wurin wata bishiya (Tree) Anan sarauniya ta runtse idanunta tana fadin wasu dalussammai. Kafin kiftawa da bismilah sai sukaga dukkanin tantunan dake wurin suna tashi sama da kansu kamar ana daga su. Su kuma sauran dakaru daganin haka sai suka nufo wurin da sarauniya take. Anan sarauniya ta musu umarni dasu tabi wannan bishiya. Ai kuwa duk wanda ya tabi bishiyar sai aga ya bace, to abun mamaki shine ko ina suke zuwa idan suka bace? Su kuwa wasu dakarun basu zo wannan wuri da sarauniya ta tsayu ba iyaka dai sun dane tantunan suna sakowa wadannan dakaru kibau. A haka tantunan suka cigaba da tashi sama tun dakarun laznun na kallonsu har suka bace, to abunda ya daurema yarima kai shine su dakarun basu nuna wani kuduri na tashi sama ba duk da cewa suna fuka fuki. Daga nan sai sarauniya ta umurci su yarima su tabi wannan bishiyar. Ai kuwa suna tabawa sai suka bace bat. Daganan sai sarauniya ta nuna wannan bishiya da dan yatsa, cikin kankanin lokaci sai bishiyar ta fara bushewa a hankali har ta zama fure daya, daukar furen tayi daga nan sai ta bace itama. Su kuwa dakarun laznun da ganin haka. Sai suka tashi suka nufi inda suka fito ba tare da sun bi bayanta ba
Sarauniya tayi mamaki da ganin dakarun sun kyaleta ba tare da sun bi bayanta ba cikin rashin sanin cewa sarki Talim ne ya basu umarni da cewa kada subi bayanta ita da mutanenta inda sun nufi su gudu, kuma bai fada musu dalilin yin haka ba iyaka dai ya basu umarni.
A lokacin da su yarima suka bace sai suka bayyana a cikin sahara, haka suma tantunan dake tashi sama sai suka bayyana a wurin. Ai kuwa basu dade da zuwa wurin ba sai ga sarauniya Munayyat ta iso. Anan tayiwa dakaru umarni dasu fara gyara tantunan domin anan zasu tsaya. Daganan sai sukaga ta fito da wani fure daya. Anan tayi tafiya mai nisa suna kallonta daga nan sai tayi gina ta rufesa. Tana rufesa sai tazo gab dasu. ” Kada ku damu nasan da cewa kuna a cikin mamaki ko? To ku sani cewa wannan fure da kuke gani shine wannan bishiyar da kuka taba har tayi sandiyar kawoku a wannan wuri. ita wannan bishiya ta kasance sihirtacciyar bishiya kuma ana kiranta da suna Bishiyar Zarma.” Anan su yarima sukayi shiru cikin mamakin wannan abu. ” Ita wannan bishiya ta kasance kamar hanya mafi saukin zuwa duk inda kakeso idan ka umarceta. Yanxu nan bada jimawa ba zakuga ta girma ta dawo yadda take.” Anan sarauniya Munayyat ta shige gaba tana musu bayani suna binta har suka iso wani tanti kayatacce. Daganan sai suka zauna suna sauraronta.
” umma inada tambaya kuma inaso ki fadamin gaskiya game da abunda kika sani, wai da gaske inada dan uwa kuwa? Inji yarima haras. Anan sarauniya tayi shiru kafin ta bashi amsa.
” Kwarai kuwa kanada dan uwa, sunansa zinam. Tare na haifeku, amma a lokacin dana haifeku sai na boyesa ba tare dana bari sarki Namil ya san dashi ba, kuma abunda yasa nayi haka shine inaso idan zanyi tafiya na tafi tare dashi kai kuwa na barka a gida. Haka itama ummin su halirat tare ta haifi diyanta wato halirat da nusaibat. To a lokacin data haifesu ne sai na sace halirat ba tare data sani ba. Kuma itama abunda yasa na saceta shine inaso nayi tafiya da ita. Nasan zakuyi mamaki abunda yasa nakeso nayi tafiya da wadannan yara ko? To ku sani cewa kafin nayi wannan tafiya sai da nayi bincike sai na gano cewa akwai wani yaro da za a haihuwa a cikin zuriar sarki Namil wato abbanka. Shi wannan yaro yanada baiwa na magana wato duk abunda ya fada to abun zai zama gaskiya koda kuwa karya yakeyi. Shi wannan yaro shine Zanim wato dan uwanka wanda na haifeku tare. Kuma a cikin wannan bincike ne na gano cewa za a haifi wata yarinya a cikin zuriar wani mafarauci mai suna Lagib. Ita wannan yarinya tanada baiwa na duk abunda ta taba da hannunta to abun zai sauya ya koma kamar yadda takeso. Ita wannan yarinya itace Halirat, kuma wannan mafarauci Lagib shine abbanta, sai kuma ga mahaifiyarta nan a kusa gareka wato Badiya.” Anan Yarima Haras ya kalli Badiya tare da diyanta biyu wato halirat da Nusaibat cikin mamaki.
” Abunda yasa nayi tafiya da wadannan yara shine domin su taimakeni gane da hadarin dake cikin wannan tafiya. Kuma a dalilinsu ne na gano duk abubuwan da nake nema. Ina fatan dai yanxu ka gansu da wannan amsa dana baka.” Inji sarauniya. Anan yarima ya gyda kai da alamar cewa E.
” To amma yanxu ina Zanim yake?” inji yarima
” Ganinan.” Anan suka juya domin suga waye ke maganar, ai kuwa anan sukayi arba da Zanim ya shigo a cikin tantin. Anan suka tarbesa cikin murna tare da karramasa. Wato Zanim ya kasance kamar an tsaga kara da yarima Haras domin kamanninsu daya, iyaka dai shi Zanim yafi kiba da kauri. Wani sauti sukaji mai hauhawa, wannan sauti yasa duk saida suka tashi suna tunani ko hari ne aka kawo. Ita kuwa sarauniya a zaune take ko zugum batayi ba.

” Kada ku damu da wannan sauti, ai wannan sauti ne na bishiyar Zarma wanda ke nuni cewa yanxu ta girma kuma za a iya amfani da ita.” Inji sarauniya. ” Yanxu ku biyoni zaku gani da idonku.” Injita. Anan suka tashi sukabi bayan sarauniya har saida sukazo dai dai wurin data binne wannan furen, ai kuwa suna duba wurin sai sukaga wannan bishiyar ta dawo. Anan suka fara mamakin wannan abu. Yanzu fa aka shukata wai har ta fito ta girma.

” To yanxu umma me zaki fada mana game da wannan bishiya ta zarma da kuma takobin Zarma?” Yarima ya tambaya yana mai duban fuskar sarauniya.

” Ita wannan bishiya..” Haka ta fada tana tabin bishiyar. ” Shekaru da dama da suka gabata, an taba yin wani sarki da ake cewa Zarma. Shi wannan sarki ya kasance yana mulkin wani birni. Mutanen wannan birni ba abunda suke in banda bautar gumaka. To wata rana rana sai wani bako ya shigo cikin garin.
Bakon ya kasance yana bin wani addini wai shi islam, to daga shigowarsa garin sai ya fara kiran jama a dasu daina bautar gumaka su riki addinin gaskiya wato islam, ai kuwa jama ar garin na ganin haka sai suka taru suka yiwa wannan mutumi duka mai tsanani suka yi masa jina jina har sai da sarki ya cecesa. To anan aka kai mutumin fadar sarki, anan sarki ya yiwa mutumin goma ta arziki tare da basa hakuri. Anan mutumin yace ba kome, bayan wasu yan lokuta kadan sai mutumin ya umarci sarki daya kaisa bayan gari domin akwai abunda zai nuna masa. Anan sarki yasa aka gyara doki daya. Mutumin aka fara azawa daganan sai sarki ya hau ya rike mutumin da hannu daya don kada ya fado sanadiyar cewa har yanxu bai warke rauninsa ba. Haka suka cigaba da gudu saman doki har suka iso bayan gari. To anan ne mutumin ya jagoranci sarki cikin wani kogo. Bayan sun shiga kogon ne sai mutumin ya dauko wani takobi ya basa tare da fada masa cewa wannan takobi zai iya tasiri ga dukkan halitta. Daga nan kuma sai ya dauko wani fure ya basa. Amfanin wannan fure shine zai iya daukarka duk inda kakeso a fadin duniyar nan. Yadda ake amfani da furen shine a shukasa. Da an shukasa cikin kankanin lokacin zai fito ya koma bishiya. Daga nan sai mutum ya fadi wasu kalamai tare da fadin duk inda yakeso ya tafi. To kana fadi sai ka tabi bishiyar. Kana tabata zaka bace iyaka ka ganka wannan wurin daka ambata. Daga nan sai bishiyar ta rikida ta koma fure ta xo wurinka. Iyaka kawai kaga fure ya fado gabanka. To bayan mutumin ya fadawa sarki haka sai ya dauko wadannan kalamai ya basa. Su wadannan kalamai a cikin wata fata suke ta zaki. Daga nan sai sarki yayi godiya. Anan sarki ya tallabosa ya aza saman doki daga nan suka nufi gari. Ba a fi sati da hakan ba sai mutumin ya mutu. Sarki yayi bakin ciki sosai da mutuwar wannan mutumi. Anan ne sarki ya fara kiran jama arsa dasu daina bautar gumaka su riki wannan addini na musulunci. To kamar yadda aka yiwa wannan mutumi shima sarki haka akaso ayi masa
Bakon ya kasance yana bin wani addini wai shi islam, to daga shigowarsa garin sai ya fara kiran jama a dadu daina bautar gumaka su riki addinin gaskiya wato islam, ai kuwa jamar garin na ganin haka sai suka taru suka yiwa wannan mutumi duka mai tsanani suka yi masa jina jina har sai da sarki ya cecesa. To anan aka kai mutumin fadar sarki, anan sarki ya yiwa mutumin goma ta arziki tare da basa hakuri. Anan mutumin yace ba kome, bayan wasu yan lokuta kadan sai mutumin ya umarci ya umarci sarki daya kaisa bayan gari domin akwai abunda zai nuna masa. Anan sarki yasa aka gyara doki daya. Mutumin aka fara azawa daganan sai sarki ya hau ya fiki mutumin da hannu daya don kada ya fado sanadiyr cewa har yanxu bai warke rauninsa ba. Haka suka cigaba da gudu saman doki har suka iso bayan gari. To anan ne mutumin ya jagoranci sarki cikin wani kogo. Bayan sun shiga kogon ne sai mutumin ya dauko wani takobi ya basa tare da fada masa cewa wannan takobi zai iya tasiri ga dukkan halitta. Daga nan kuma sai ya dauko wani fure ya basa. Amfanin wannan fure shine zai iya daukarka duk inda kakeso a fadin duniyar nan. Yadda ake amfani da furen shine a shukasa. Da an shukasa cikin kankanin lokacin zai fito ya koma bishiya. Daga nan sai mutum ya fadi wasu kalamai tare da fadin duk inda kakeso ka tafi. To kana fadi sai ka tabi bishiyar. Kana tabata zaka bace iyaka ka ganka wannan wurin daka ambata. Daga nan sai bishiyar ta rikida ta koma fure ta xo wurinka. Iyaka kawai kaga fure ya fado gabanka. To bayan mutumin ya fadawa sarki haka sai ya dauko wadannan kalamai ya basa. Su wadannan kalamai a cikin wata fata suke ta zaki. Daga nan sai sarki yayi godiya. Anan sarki ya tallabosa ya aza saman doki daga nan suka nufi gari. Ba a fi sati da hakan ba sai mutumin ya mutu. Sarki yayi bakin ciki sosai da mutuwar wannan mutumi. Anan ne sarki ya fara kiran jama arsa dasu daina bautar gumaka su riki wannan addini na musulunci. To kamar yadda aka yiwa wannan mutumi shima sarki haka akaso ayi masa saida mabiyansa wadanda suka karbi addinin Islam suka karesa. To a cikin dare na wannan rana ne wani bala i ya afkama garin. Wani bakin hadari ne aka buga daga nan aka fara zazzago ruwan duwatsu. Su wadannan duwatsu manya manya ne masu ci da wuta yadda idan daya ya fado zai iya lalata gidaje dari. A duk lokaci da daya ya fado to sai mutane fiye da dubu sun mutu. To anan ne sarki ya dauko furensa ya shuka, cikin kankanen lokaci furen ya koma bishiya. Daga nan sai ya dauko fatar zaki mai dauke da kalaman ya fara karantawa. Bayan ya karanta ne sai ya ambaci inda yakeso ya tafi.Cikin sauri ya fara kiran jama arsa da suxo su tabi wannan bishiya domin subar garin. Ai kuwa anan jama a suka sheko a guje da nufin tabin bishiyar. To abun mamakin daya faru shine duk mutumin da bai yi imani da addinin musulunci ba daya nufi wurin bishiyar sai aga wani iska mai karfi ya dagasa ya masa guntu guntu wato kai daban, hannaye daban hakama kafufuwa daban. Haka wannan bala i yaci gaba da gudana har sai da dukkanin jama ar garin suka mutu. Mabiya addinin musulunci ne kawai suka tsira wato sarki da wasu yan kalilan. Sarki Zamra tare da mutanensa sun isa wani wuri mai ni ima da daushin kasa. Ana suka kafa sabon garinsu mai suna Ganduje. Shi kuwa wannan takobi da fure sai aka kaisu a gidan tarihi na garin aka ajiye tare da rubuta wannan labari dana baku a cikin wannan fatar da zaki da mutumin yaba sarki Zamra. Daga nan kuma aka samu dakaru masu gadin takobin da fure a ko yaushe. Haka aka cigaba da kula da wannan takobi da fure zamani zuwa zamani har aka kawo ga sarkin ganduje na yanxu wato sarki ajib, shi kuwa sarki ajib fiye da shekara goma da suka wuce wani sarki ya kawo masa harin sumame ya kwace takobin da fure.

Shi wannan sarki daya kwace takobin yana daya cikin sarakuna goma na kungiyar sarki Talim, sunansa Midal, ni kuwa dana tashi sai na kai masa ziyarar ba zata nima na sace takobin da kuma furen. Wannan labari shine asalin takobin zarma kuma shine asalin bishiyar zarma.” Inji sarauniya Munayyat.

” To yanzu umma ya za ayi mu kare birninmu da kuma kanmu game da wadannan dakaru na laznun?” Yarima Haras ya tambaya.

“Ai hanya biyu ce kawai, yanzu mu koma tanti tukuna.” Anan sukabi bayan sarauniya har suka iso tanti. To bayan sun zauna ne sai sarauniya ta cigaba da bayani. ” Kamar yadda na fada hanya biyu ce, ta farko itace muyi amfani da takobin Zarma domin yakan yi tasiri ga jikin dakarun Laznun. Hakama duk wani azzalumi idan aka fuskancesa da wannan takobi bako shakka sai anga bayansa. Hanya ta biyu kuwa itace mu koma birnin Ganduje da zama sabida na dade da samun tabbaci cewa abunda suke bautawa shine gaskiya kuma inaga muma idan mukayi irin bautar da sukeyi bako shakka zamu samu kariya.”

” Ni a ganina kara mubi dukkan wadannan hanyoyin ma ana mu koma birnin ganduje da zama kuma muyi amfani da takobin wurin yakarsu idan sun kawo mana farmaki.” Inji Badiya.

” Kinada gaskiya amma fa kada ki manta muma munada birni, to ni a ganina me zai hana muje mu koyi addininsu idan yaso sai mu koma garinmu mu cigaba da yin irin abunda sukeyi.” Inji yarima Zanim.

Anan sarauniya ta fita waje su kuwa kowanensu sai fadin albarkacin bakinsa yake, ai kuwa sarauniya na fita kawai sai sukaji ihu da karajin mutane kamar wani abu ya faru. To anan ne suka fito da sauri domin ganin kome ke faruwa kawai sai sukaga daya daga cikin dakarun Laznun ne ya dauke sarauniya yayi sama da ita su kuwa sauran dakaru sai halbinsa suke da kibau amma duk a banza. Ita kuwa sarauniya cikin gwaninta ta dauko takobin Zarma dake rataye a kugunta ta fara yakarsa. A duk lokacin data kai masa sara yakan kauce ba tare da saran ya kai ga jikinsa ba. Haka suka cigaba da wannan artabu a sararin samaniya har sai da sarauniya ta fara gajiya. To anan ne ya samu nasarar yi mata wani naushi a fuska. Nan take ta saki takobin ta rikito kasa shi kuwa da sauri ya kwace takobin ya tafiyarsa. Kafin sarauniya ta fado kasa sai wasu dakarun suka tara hannayensu tana fadowa suka cabeta. Anan aka shiga da ita cikin tanti ana mata magani. Bayan sarauniya ta samu sauki sosai sai ta mike cikin fushi. Anan ta fara shirin yaki ita kadai. ” Wai wannan shiri da kike lafiya kuwa?” Badiya ta tambaya

” Ai ba lafiya domin yanxu zan dawo da wannan takobin, inada tabbacin cewa sarki Talim ne ya aikosa sabida haka yanzu kinga tafiyata.” Inji sarauniya

” Ai kuwa indai hakane nima ina bayanki domin tare zamu.” Inji badiya. Anan sarauniya tayi shiru, can sai ga shugaban dakaru ya shigo tare da nusaibat da zanim. To bayan sunji kadurin sarauniya munayyat sai suka goyi bayanta tare da daukar niyar binta. Yarima Haras da Halirat aka bari su ci gaba da shugabancin dakarun kafin su dawo, su kuwa cikin sauri sukabi ta bishiyar Zarma da nufin zuwa birnin sarki Talim wato Asmariya. To kafin su tafi ne sarauniya taba Yarima Haras wata tsuntsuwa. Anan ta fada masa cewa da yaga tsuntsuwar ta mutu to suna cikin matsala sabida haka yayi sauri ya kawo musu agajin gaggawa.

Ai kuwa cikin wannan dare wannan tsuntsuwar da akaba yarima i ta mutu. To anan ne ya gane cewa bako shakka su sarauniya na cikin wani yanayi. To anan ne ya kira Halirat domin ta bada shawara yadda zasu bulloma al amarin.

“Ni inaga kawai mu tafi mu nemi taimakon sarki ajib na birnin Ganduje tare da fada masa cewa idan an samu nasara xamu basa takobin tunda shima yana nemansa.”Inji Halirat. Anan yarima ya karbi wannan shawara. Safiya na wayewa suka dau hanya shida sauran dakaru, kwanci tashi har suka iso birnin ganduje, to bayan sun iso ne sai suka yiwa sarki bayanin abunda ke tafe dasu. Ai kuwa kai tsaye ya aminta. Anan yasa akayi shelar yaki ciki da wajen gari. Kafin kaceme fiye da dakaru dubu saba in sun gabato. Anan suka jero sahu sahu rike da muggan makamai. Daga nan sai aka bude kofar fita gari. Saman dawakai wadannan dakaru suka fito a guje suka nufi birnin sarki Talim. Kwanci tashi har suka iso. To daga nan ne yarima Haras ya tsara yadda za a gudanar da yakin cikin salo, wato da farko shi zai fara shiga cikin garin tare da Halirat su nemo inda aka ajiye takobin Zarma idan yaso daga baya sai su bude ma sauran dakaru kofar garin. Anan sarki Ajib ya yarda da wannan shawarar amma da sharadin shima zai bisu. Daga nan suka nufi kofar shiga garin. A wannan lokaci da dare ne, to bayan sun shiga garin ne sai suka nufi masarautar kai tsaye. Ga masu gadi amma duk bacci suke. A nan suka fara binciken masarautar lungu lungu sako sako har suka iso turakar sarki Talim. To anan ne sukaga takobin Zarma rataye da kugunsa yana bacci suma dakarun dake gadinsa baccin suke. To anan ne suka samu damar kwace takobin a hankali ba tare daya farka ba. Daga nan suka nufi gidan yari. Suna zuwa suka tarar da dakarun dake gadin wurin duk suna bacci. Anan suka kwace makullen suka bude wurin. Ai kuwa suna budewa sai sukayi arba da su sarauniya duk sun jigata. Shi kuwa Yarima Haras anan yayi arba da abbansa sarki Namili. Wato bayan birnin su ya fadi anan aka kawosa a matsayin fursuna. Anan suka kwancesu tare da basu makamai domin su kare kansu. To a cikin wadanda suka kwance sai Halirat taga wata bakuwar fuska ta wani dattijo. Anan ta nemi sanin koshi waye. Anan ne Badiya ta fada mata cewa ai shine mahaifinta Lagib, wato a lokacin da Halirat ta bace shi kuma sai ya shiga duniya nemanta. Haka yayita yawo har ya iso birnin sarki Talim inda aka kamasa ana azabtar dashi a matsayin bawa. Anan Halirat ta sheko ta rungumesa cikin farin cikin haduwa dashi. Daga nan sai suka nufi hanyar fita domin su budewa sauran dakaru kofar gari. Ai kuwa suna kaiwa bakin kofar sai sukaga da yawa daga cikin dakarun sarki Talim sun farka. To anan ne aka fara kallon kallon kafin su kaceme da azabben yaki. Ana cikin wannan gumurzu ne sarki ajib ya mamayi sauran dakaru ya bude kubobin kofar garin, daga nan ya hura wata mabusa mai kara wadda itake fadawa dakarunsa cewa su karaso. Ai kuwa cikin kankanin lokaci ne suka shigo cikin garin da azababben gudu. To a wannan lokaci sarki Talim ya farka hakama dukkanin dakarunsa sun farka. Daga nan ya bada umarni a kwance dakarun Laznun domin suma su shigo wannan yaki. Abinka da matsafi cikin sauri ya turawa sauran abokansa yan kungiya da cewa suzo da dakarunsu domin suma a gwabza dasu. Cikin kankanin lokaci suka iso sabida suna amfani da tsafi. To bayan isowar wadannan sarakuna su takwas tare da dakarunsu sai yaki ya koma sabo sabida sunfi dakarun sarki ajib yawa nesa ba kusa ba. A wannan lokaci yaki yayi yaki duk inda ka duba sai karar takubba kakeji da gawawwakin wadanda aka kashe. Cikin dubara da salo na yaki sarki Ajib yayiwa dakarunsa umarni dasu dukufa wurin yin addua. Daga nan sai wasu daga cikinsu suka daga hannyensu sama suna addu a su kuwa saura suka cigaba da yaki suna ba masu yin adduar kariya. Basu wani dadewa da fara adduar ba sai sukaga sama ta canza tayi baki kirin.

Daga nan sai aka fara iska mai tsananin karfi, shi dai wannan iska da ban mamaki yake domin daukar dakarun su sarki Talim yake yana musu guntu guntu, su kuwa dakarun sarki ajib ko kadan basajin iskan. Daga nan kuma sai aka fara yin ruwan duwatsu masu ci da wuta, cikin kankanin lokaci aka karar da rundunar wadannan sarakuna su tara dasu kansu, sabida daya bayan daya iskan yayita hallakasu har suka mutu gaba daya. Daga nan sai dakarun sarki Ajib suka fara ihu na samun nasara tare da godewa ALLAH. Daga nan akaba sarki Ajib takobin Zarma da kuma furen Zarma domin ya mayar dasu gidan tarihi. Su kuwa su Yarima Haras tare suka koma birninsu na Ganya. Anan mutanen gari suka tarbesu cikin karramawa, sarki Namil dai ya koma kan kujerarsa ta mulki tare da sarauniyarsa Munayyat, shi kuwa Yarima Haras sai ya auri Halirat, shi kuwa yarima Zanim sai ya auri nusaibat. Lagib kuwa ya ci gaba da zama da matarsa Badiyat. Wannan shine karshen labarin Takobin Zarma
The End
Alhamdulillah
Written by Abdul King Article

Leave a comment